Type Here to Get Search Results !

Abun mamaki: Maciji gama sheka ya mutu bayan wani yaro dan shekara takwas ya cije shi a Indiya

Abun mamaki: Maciji gama sheka ya mutu bayan wani yaro dan shekara takwas ya cije shi a Indiya


Wani yaro dan shekara takwas a Indiya ya firgita mutane da yawa bayan ya kashe wani maciji da ta nade kanta a hannu.

An bayyana cewa yaron mai suna Deepak, ya cije macijin bayan ta nade kanta a kusa da shi a lokacin da yake wasa a lambun gidansu da ke kauyen Pandrapath a Chhattisgarh ranar Litinin

Kamar yadda Mail Online ya ruwaito, macijin ya kama shi ne a lokacin da yake wasa a wajen gidansu, kuma ya raunata jikinsa a hannu. 

Da yake fama da ciwon, Deepak ya fusata ya girgiza hannunsa amma ya kasa sakin macijin da ya nade hannunsa, inda a nan ne yaron ya ciji macijin da hakoransa.

"Macijin ya nade hannuna ya sare ni.  Na ji zafi sosai,' Deepak ya shaida wa New Indian Express.

"Na yi ƙoƙarin girgiza shi, na ciji shi da ƙarfi sau biyu.  Duk abin ya faru a cikin walƙiya,' in ji shi.

Daga bisani iyayen yaron suka garzaya da shi wata cibiyar kula da lafiya da ke kusa da shi inda aka sanya masa ido domin ganin ya samu sauki.

Binciken raunin da ya samu ya sa likitoci suka gano cewa macijin ya yi masa busashshen cizo, ma’ana ba ta saki wani dafi ba.

"Deepak bai nuna alamun cutar ba kuma ya murmure cikin sauri saboda busasshen cizon da macijin ya yi amma ba a saki dafin ba," in ji wani kwararre kan maciji da New Indian Express.

Post a Comment

0 Comments
* Please Don't Spam Here. All the Comments are Reviewed by Admin.

Top Post Ad

Below Post Ad

Hollywood Movies