Da dumi-dumi: An damke dan Luwadi bayan ya taushe yaro dan shekara 5 ya yi masa ludu har ya mutu, ya kuma gina rami ya binne shi


Rundunar ‘yan sandan jihar Ogun a ranar Juma’a, 25 ga watan Nuwamba ta kama wani dan luwadi dan shekara 36 mai suna Sikiru Ajibola bisa zargin yi wa wani yaro dan shekara 5 fyade har lahira a yankin Ogijo na jihar Ogun.

An kama wanda ake zargin ne biyo bayan rahoton da shugaban CDA na Olorunwa Arogbeja Ogijo ya gabatar a hedikwatar Ogijo, wanda ya bayyana cewa daya daga cikin al’ummar yankin ya sanar da shi cewa wanda ake zargin ya yi Luwadi da wani yaro Dan shekara 5, sakamakon haka yaron ya mutu.

Bayan rahoton, DPO reshen Ogijo, CSP Enatufe Omoh, ya yi gaggawar jagorantar jami’an bincikensa zuwa inda lamarin ya faru inda nan take aka cafke wanda ake zargin.  A lokacin da ake yi masa tambayoyi, wanda ake zargin ya amsa laifinsa cewa shi dan luwadi ne kuma yayin da yake yiwa yaron da ya rasu fyade, yaron ya mutu.

Ya kara da cewa ya yi gaggawar tona wani kabari mara zurfi a wani daji da ke kusa, inda ya binne yaron.

Ya kuma kai ‘yan sanda inda aka binne mamacin.

Da yake tabbatar da faruwar lamarin, kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, SP Abimbola Oyeyemi, ya ce kwamishinan ‘yan sandan jihar, CP Lanre Bankole, ya bayar da umarnin mika lamarin ga sashen binciken kisan gilla na sashin binciken manyan laifuka na jihar domin ci gaba da bincike da kuma tabbatar da tuhumar wanda aka kama. 

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN