Atiku butulu ne, bai da rana: Tinubu ya sake biyowa ta kan abokin hamayyarsa


Asiwaju Ahmed Bola Ahmed Tinubu, dan takaran kujerar shugaban kasa karkashin jam'iyyar All Progressives Congress (APC), ya sake dira kan abokin hamayyarsa na jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP), Alhaji Atiku Abubakar. Legit.ng ta ruwaito.

Tinubu ya ce Atiku Butulu ne tunda har yake kokarin takara da shi a zaben 2023, rahoton DailyTrust.

Tinubu a wajen taron yakin neman zabensa da ya gudana ranar Asabar, 26 ga Nuwamba a filin Teslim Balogun dake Legas, ya yi kira ga jama'a su yiwa Atiku ritaya da katin zabensu a 2023 saboda ya daina takara.

Ya yi alkawarin cewa zai cigaba daga inda shugaba Buhari ya tsaya kuma za'a dama da kowa.

Yace:

"Yayi takara karkashin PDP. Ya yi takara karkashin ACN, mun karbeshi hannu biyu-biyu. Butulu ne. Bai kamata ya sake takara ba. Kuyi amfani da kuri'unku kuyi masa ritaya."

Wai Sau Nawa Atiku Zai Yi Takara Ne? Ku Fada Masa Yaje Ya Huta: Cewar Tinubu

A jiya, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu ya biyo ta kan Alhaji Atiku Abubakar yayinda ya tafi yakin neman zabensa masarautar Gbaramatu dake jihar Delta.

Tinubu ya shawarci Atiku tunda ya dade yana neman wannan mulki kuma har yanzu bai samu ba kawai ya hakura kuma ya janye.

Tinubu ya yiwa Atiku isgili wai shin sau nawa zai yi takara.

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN