Zargin wulakanta gawa: An gurfanar da mutane biyu gaban Kotu


Wasu mutane biyu masu suna Isah Abdulkabir da Daniel Emmanuel sun gurfana a gaban wata kotun majistare ta jihar Oyo da ke Iyaganku, Ibadan, ta hannun ‘yan sanda, bisa zargin su da hannu wajen wulakanta gawar wani Patrick Alexandra
.

Wadanda ake tuhuman da aka gurfanar da su a gaban kuliya bisa tuhumar da suka shafi hada baki da kuma rashin da’a ta hanyar ‘wulakanta gawa’, sun aikata laifin ne da misalin karfe 2 na rana a ranar 19 ga Satumba, 2022, a unguwar Odogbo da ke Ibadan

‘Dan sanda mai shigar da kara, Foluke Adedosu, ya ce wadanda ake zargin sun wulakanta gawar ta hanyar jefa ta a cikin shago, laifin da ya saba wa sashe na 516 da 242 (1) (b) na dokokin laifuka na jihar Oyo, 2000.

Bayan wadanda ake zargin sun musanta aikata laifin.  Alkalin kotun, O.A.  Enilolobo, ya amince da bayar da belinsu a kan kudi Naira 100,000 kowannensu tare da masu tsaya masu. 

An dage ci gaba da sauraren karar har zuwa ranar 21 ga Fabrairu, 2023.

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN