Babu wani shiri na sake haramta duk wani dandalin sada zumunta a Najeriya, amma... - FG

Babu wani shiri na sake haramta duk wani dandalin sada zumunta a Najeriya, amma... - FG


Gwamnatin Najeriya ta ce ba ta da niyyar sake haramta duk wani dandalin sada zumunta a kasar.

Ministan yada labaran kasar, Alhajir Lai Mohammed ne ya bayyana haka a wani taron manema labarai a Abuja ranar Alhamis.

A cewar Ministan, gwamnatin tarayya ba za ta zauna ta kyale duk wani dandali da zai jefa al’ummarmu cikin mawuyacin hali ba.

Koyaya, gwamnati ta lura cewa za ta ci gaba da sa ido kan abubuwan da ke faruwa a dandalin microblogging, Twitter, bayan wani sabon mai shi ya karbe shi.

Ministan ya ce dakatar da dandalin a shekarar da ta gabata ya samo asali ne saboda ra'ayin da wasu suka yi na amfani da shi wajen hargitsa Najeriya ta hanyar labaran karya da kuma kalaman kiyayya.

Mohammed ya yi gargadin cewa gwamnati ba ta da niyyar haramtawa duk wani kafafen yada labarai gudanar da ayyukanta, haka kuma ba za ta bari a yi amfani da duk wata hanyar da za ta jefa kasar cikin rikici ba.

Previous Post Next Post

Latsa nan domin samun labaran mu ta WhatsApp kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilin mu a garin ku LATSA NAN

Domin aiko rahotu/ korafi LATSA NAN

Domin samun labaran mu a Facebook LATSA NAN ka danna FOLLOW ko LIKE