An kama jami'in hulda da jama'a na ISWAP a kasuwar Kaduna
Sojoji sun kama wani da ake zargin dan kungiyar Islamic State in West Africa Province (ISWAP) a jihar Kaduna.
Zagazola Makama, wani wallafi da ya mayar da hankali kan yankin tafkin Chadi ya ce wanda ake zargin mai suna Nasiru Mohammed, ana zarginsa da bayar da mafaka ga ‘yan ta’addan da ke tserewa daga arewa maso gabas.
Matsugunin na taimaka musu su zauna kafin a kai su wasu sansanoni a arewa maso yamma da tsakiyar kasar.
Mohammed wanda kuma ke taimakawa ‘yan ta’addan da kayan aiki yana aiki ne a reshen GSM na tsakiyar kasuwar Kaduna kafin a kama shi.
Rubuta ra ayin ka