Yadda yaro na ya taɓa ƙoƙarin gabatar da ni ga maita don samun arziki - Jaruma

Yadda yaro na ya taɓa ƙoƙarin gabatar da ni ga maita don samun arziki - Jaruma


Fitacciyar jarumar fina-finan Najeriya ta koma mai wa'azi, Idowu Phillips wanda aka fi sani da Mama Rainbow ta bayyana yadda daya daga cikin ‘ya’yanta ya taba kokarin shawo kan ta ta zama mayya domin ta samu arziki.

A hirarta da Daily trust, jarumar ta bayyana cewa ta samu karyewa ne tun a matakin farko na sana’arta, musamman ganin mijinta, Femi ya rasu bayan shekaru kadan da aurensu, inda ta yi renon ‘ya’yansu.

Mama Rainbow ta tuna yadda ɗaya daga cikin 'ya'yanta waɗanda tun farko ba su daidaita da aƙidunta ba,  ya ba da shawarar cewa ta zama mayya don su zama masu arziki.

Ta ce;

“Yana da wuya;  bayan sallah wasu sai kuka sukeyi.  Duk lokacin da daya daga cikin ’ya’yana ya gan ni da Littafi Mai Tsarki yakan tambaye ni abin da nake yi da shi.  A wani lokaci, ya ce zai kai ni inda zan zama mayya, na yarda.  Ya ce da zarar na zama mayya za mu yi lafiya.”

Mama Rainbow ta kara bayyanawa bayan tayi sallama ta nufi wajen, danta ya ja ta suka fice daga wajen bayan ya fahimci farashin da ke tattare da lamarin.

Ta kara da cewa;

“Na yarda sai ya kai ni wani wuri, amma a gaban Allah da mutum, da na isa wurin suka gaya mini abubuwan da ake bukata, sai na yi mamaki.  Suka ce yaron da na fi so shi ne za a yi amfani da shi don sadaukarwa.

“Na gaya wa mutumin cewa yaron da na fi so ne ya kawo ni wurin.  A lokacin, dana ya rike hannuna ya ce lokaci ya yi da zan koma gida.

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN