IGP ya maida Kwamishinan yan sandan Kano zuwa Ebonyi bisa zargin almundahana

IGP ya maida Kwamishinan yan sandan Kano zuwa Ebonyi bisa zargin almundahana

CP Abubakar Lawal

Babban sufeton ‘yan sandan Najeriya Alkali Usman ya mayar da kwamishinan ‘yan sandan jihar Kano Abubakar Lawal aiki zuwa jihar Ebonyi, biyo bayan zargin cin hanci da wasu manyan jami’an ‘yan sandan jihar suka yi masa.

A wata siga mai lamba: TH.5361/FS/FHQ/ABJ/V.T3/87 da aka saki da yammacin Juma’a, IGP ya tura kwamishinan ‘yan sandan jihar Ebonyi Aliyu Garba domin ya maye gurbin Mista Usman nan take.

Jaridar DAILY NIGERIAN ta tattaro cewa wasu manyan jami’an ‘yan sanda a hukumar ‘yan sandan jihar Kano sun koka kan yadda CP ke aikata almundahana, lamarin da ya sa IGP ya bayar da umarnin gudanar da bincike mai zurfi kan zargin.

Wasu majiyoyin da ke da masaniya kan lamarin sun kuma ce IGP din ya kuma nemi ganawa da wasu jami’an rundunar da kansa, wadanda suka tabbatar da zargin da ake yi wa CP.

Sabon kwamishinan ‘yan sandan Kano ya kammala karatun digiri na BA History a Jami’ar Sakkwato, kuma ya yi digirin digirgir a fannin shari’a da diflomasiyya a Jami’ar Kimiyya da Fasaha ta Port-Harcourt, Jihar Ribas.

Sabon CP Aliyu Garba

Ya shiga aikin ‘yan sandan Najeriya ne a shekarar 1990 a matsayin mataimakin Sufeto na ‘yan sanda, Cadet ASP, a makarantar ‘yan sanda (Annex) Jihar Kaduna, inda ya yi horo na tsawon watanni 18 sannan aka tura shi rundunar ‘yan sandan jihar Oyo a matsayin Admin Officer.

Daga nan kuma sai aka mayar da shi Rundunar Jihar Neja a shekarar 1992 inda ya zama ADC ga Gwamnan Jihar Neja a lokacin, Musa Inuwa.

Malam Garba ya yi aiki a bangarori daban-daban na rundunar, ya kuma halarci kwasa-kwasan kwararru da dama a fannin bin doka da oda, hana aikata laifuka da gudanar da ayyuka a ciki da wajen kasar nan.

Ya taba zama mataimakin kwamishinan walwala na ‘yan sanda, sashen kudi da mulki, hedkwatar rundunar da ke Abuja, hedkwatar rundunar bincike da tsare-tsare ta DCP, Abuja, mataimakin kwamishinan ‘yan sanda na shiyyar 2 da ke Legas.

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN