Zaben 2023: Da gaske Atiku munafiki ne? Dan takarar PDP ya gamu da wata babbar badakala a kan faifan bidiyo
Dan takarar babbar jam’iyyar adawa ta PDP, Atiku Abubakar ya fuskanci suka sosai biyo bayan wani kalami da ya yi wanda ake ganin ya nuna kabilanci a lokacin da yake zantawa da wani kwamitin hadin gwiwa na Arewa a Kaduna a karshen mako.
Kamar yadda jaridar Punch ta ruwaito, dan siyasar wanda haifaffen Adamawa ne a yayin zaman tattaunawar ya ce bai kamata yankin arewa su zabe shi ba saboda ya fito daga arewa.
Ya kuma bayyana cewa, kada su zabi dan kabilar Ibo ko Yarbawa, kalaman da ke nuni da dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar Labour, Peter Obi, da na jam’iyyar All Progressives Congress (APC), Bola Ahmed Tinubu.
A cikin fadinsa, ya ce:
Abin da talakawan Arewa ke bukata shi ne wanda ya fito daga Arewa kuma ya fahimci wani bangare na kasar nan kuma ya iya gina gadoji a fadin kasar nan.
“Wannan shi ne abin da dan Arewa yake bukata. Ba ya bukatar dan takarar Yarbawa ko Igbo. Na tsaya a gabanka a matsayin dan Najeriya dan asalin arewa.''