GWAMNA BALA MOHAMMED YA YI AFUWA GA 'YAN FIRSINA 153 A JIHAR BAUCHI

 GWAMNA BALA MOHAMMED YA YI AFUWA GA 'YAN FIRSINA 153 A JIHAR BAUCHI

Daga Muazu Hardawa a Bauchi


A kokarin sa na ganin kowane mutum ya ci gajiyar ayyukan Alheri da gwamnati ke aiwatarwa, Gwamna Bala Mohammed Abdulkadir na Jihar Bauchi ya Yi ahuwa ga daurarrun Firsinoni 153 da ke zaman wakafi a gidajen yari 13 a fadin Jihar Bauchi domin rage cunkoso a gidajen gyaran tarbiyyar.

Cikin wani biki da aka gudanar a gidan gwamnati ranar juma'a, gwamna Bala Mohammed ya bayyana jin dadin sa ga mutanen da suka samu 'yancin su a wannan rana inda ya ce ahuwar ta biyo bayan irin shawarwarin da mahukunta suka bayar ne game da yadda doka ta ba shi damar yin afuwar ta hanyar lura da lafiya ko tsufa ko biyan tara ga mutanen da suka ci moriyar shirin.

Kwamishinan sharia na jihar Bauchi kuma shugaban kwamitin yin afuwa ga firsinonin Alhaji Abubakar Abdulhamid Bununu cikin jawabinsa ya bayyana cewa aikin yin afuwar na cikin doka ta 212 inda tsarin Mulki ya bayar da dama ga gwamna na tausayawa wajen yin afuwa ga wanda laifin sa bai taka kara ya karya ba. Kuma an bi dukkan sharuddan da suka dace domin tausayawa daurarrun wajen biya musu tara da bata taka kara ta karya ba kuma idan ya kasance laifuka ne da za a iya musu afuwa.

Babbar Mai shari'a ta Jihar Bauchi Hajiya Rabi Talatu Umar ta yaba da kokarin gwamnatin Sanata Bala Mohammed Abdulkadir na bayar da damar sakin mutane 153 daga gidan yari daban daban na Jihar Bauchi. Inda tace a karkashin doka itama ofishin ta na zagaya gidajen yari tana duba irin shari'a da alkalai ke yi kuma tana sake Wanda taga ana tsare da su ba bisa Ka'idaba ko Wanda suka zauna fiye da adadin da ya kamata su kasance a gidan gyaran tarbiyyar.

Hajiya Rabi Talatu Umar ta roki yafaffun masu zaman wakafin su gyara halayen su ta hanyar zaman lafiya da kowa tare da neman abin yi na kwarai don ganin basu sake dawowa wannan gida na.gyaran tarbiyya ba.

Shima kakakin majalisar dokokin Jihar Bauchi Alhaji Abubakar Sulaiman ya bayyana cewa Sakin mutane 153 babban aiki ne da ya kamata a yaba, don haka ya ja hankalin wanda suka ci gajiyar ahuwar ya zamo darasi a garesu ta hanyar nisantar aikata laifuka idan sun koma garuruwan su. 

Alhaji Ali Abubakar Bajoga kwantirolan hukumar gyaran hali ta Bauchi cikin jawabinsa ya bayyana farin ciki game da wannan aiki wanda zai taimaka musu wajen rage cunkoso a gidajen gyaran tarbiyya. Don haka yace sakin mutane 153 shine mafi girma da wani gwamna ya yi a Nigeria cikin sama da shekaru ashirin da ya san ana irin wannan afuwa. 

Inda ya Kara da cewa hatta shugaban hukumar gidan gyaran tarbiyya na kasa Alhaji Halliru Nababa Shima ya yaba game da wannan aiki da gwamnan ya aiwatar don zai taimakawa hukumar inganta ayyukan ta.

Yace koyar da sana'a na cikin manyan ayyukan da suke yi a gidan gyaran tarbiyya don ganin duk Wanda ya shiga wannan gida idan ya samu 'yancin fita ya samu hanyar dogaro da kansa daga Sana'a da ya koya.

 Don haka suka bayar da kyautar hula da takalmin da suka yi a gidan gyaran tarbiyyar kuma nan take gwamna Bala Mohammed Abdulkadir ya cire takalmi da hular sa ya sanya Wanda suka bashi.

Ahmed Adamu da Umar Yau da Zulkallaini Adamu da Aliyu Usman da wasu daga cikin su na cikin wanda gwamna ya musu ahuwa Kuma ya basu kudin da za su koma gida su ja jari.

Saidu Adamu Giyade cikin jawabinsa na godiya a madadin wanda suka samu ahuwar yace shekararsa takwas da watanni  a gidan yarin saboda rabiyar fada ya abka cikin wannan kaddara don haka yace zamansa a wannan gida ya haddace Kur,ani izu 60, don haka ya gode da wannan ahuwa da aka masa tare da ba shi naira dubu 50 don ya ja jari, Amma zai je ya dinkawa matarsa da yaransa kayan sawa ne da kudin kuma ya sayi nama yaci don yayi kala'i saboda ya jima bai ci nama ba.

Kuma ya roki 'yan siyasa su taimaka masa saboda shima ya yi hidimar siyasa a baya kuma yanzu yana son jari don kama Sana'a.

Nan take shugaban karamar hukumar Giyade Alhaji Abubakar Mohammed da Alhaji Abubakar Faggo kowane cikin su ya ba shi kyautar mashin. 

Ahuwar ta shafi daurarru daga dukkan gidajen yari na Bauchi da Jamaare da Misau da Azare da Ningi da Alkaleri da Zaki da Darazo da Bogoro da Nabordo da Burra da Gamawa da sauran su.

Bayan kammàla ba su kudin tallafi na naira dubu 50 ga mutane 50, gwamna Bala Mohammed ya bayyana cewa ya musu afuwa ce a karkashin doka ta 212 wacce ta bashi damar duba zaman da mutane suka yi a gidan gyaran tarbiyyar. Bayan dukkan tuntubar mahukunta da kwamitin yafiya da tausayawa da aka kafa ya lura da yadda aikin ya gudana wajen biyan tarar da bata wuce duba talatin ba ko diyyar da bata wuce dubu biyar ko goma ba, tare da lura da rashin lafiya ko tsufa da daurarrun ke fama da shi, inda ya biya sama da naira milyan daya da dubu Dari biyu a matsayin tara ko diyyar musu afuwar.

Sanata Bala Mohammed ya bayyana cewa hakkinsa ne ya dubi halin da daurarrun suke ciki musamman Wanda suka shekara biyu ko uku ko Kuma suka gaza biyan tarar da bata taka kara ta karya ba don haka ya zamo wajiba a matsayin sa na wanda Allah ya ba jagoranci na Jihar BauchiI ya dubi matsaloli na talakawa da marasa galihu a kowane matakin don yi musu abin da ya dace don a fita hakkin kowa.

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN