An kama kawun wani yaro tare da mutane biyar da suka dinga Luwadi da yaron dan shekara 7 a Sokoto

An kama kawun wani yaro tare da mutane biyar da suka dinga Luwadi da yaron dan shekara 7 a Sokoto


Hukumar tsaron farin kaya ta Najeriya (NSCDC) reshen jihar Sokoto ta kama wasu mutane biyar da suka yi wa wani yaro dan shekara 7 fyade tare da luwadi da su.

Da yake zantawa da manema labarai yayin da yake gabatar da wadanda ake zargin a hedikwatar rundunar da ke Sokoto, Kwamandan jihar, Mohammed Saleh-Dada ya ce daya daga cikin wadanda ake zargin kawun yaro da aka yi ma luwadi ne.

Ya ce kawun shi ne wanda ake zargi na farko da ya yi wa karamin yaron fyade sannan kuma ya gayyaci wasu mutane hudu da suka rika yi wa yaron fyade har sai da suka lalata masa muhimmin yankinsa.

Kwamandan ya kuma bayyana cewa rundunar tana kuma gurfanar da wanda ake zargi da laifin yiwa wata yarinya ‘yar shekara biyar fyade da ke da alaka da shi.

A cewarsa, an tasa keyar wanda ake zargin zuwa gidan yari bayan zaman Kotu.

Ya ce rundunar ta kuma samu umarnin Kotu na ci gaba da tsare mutanen biyar da ake zargi da yin luwadi da su domin kammala bincike kan lamarinsu kafin a sake gurfanar da su a gaban Kotu.

A halin da ake ciki, Kwamandan ya roki lauyoyi da sauran masu fafutukar kare hakkin bil’adama da su rika la’akari da wadanda aka cuta wa da kuma alakar su a koda yaushe kafin gabatar da karar wadanda ake zargi da aikata laifukan fyade da luwadi.

Ya ce ba za a iya tunanin irin raunin da irin wadannan mutane ke ciki da alakarsu ba.

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN