Yanzu yanzu: Rikici ya barke, an yi arangama tsakanin yan iskan Agbero da yan kasuwa a kasuwar Alaba da ke Lagos, an raunata da dama (Bidiyo)

Yanzu yanzu: Rikici ya barke, an yi arangama tsakanin yan iskan Agbero da yan kasuwa a kasuwar Alaba da ke Lagos, an raunata da dama (Bidiyo)
A safiyar yau 19 ga watan Oktoba ne rikici ya barke a babbar kasuwar Alaba International Market da ke Legas, yayin da ‘yan kasuwa suka yi arangama da yan iska a yankin. Shafin labarai na isyaku.com ya samo.

Rahotannin da ba a tabbatar da su ba sun ce ‘yan kasuwar sun nuna adawa da bukatar kudi da yaran yankin da aka fi sani da Agberos ke yi a yankin.

Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Legas, SP Benjamin Hundeyin, ya ce ‘yan sandan na kokarin dawo da zaman lafiya a yankin.

An kai wasu mutanen da suka samu raunuka a wannan tabarbarewar yanayi asibiti domin yi musu magani. 

Duba bidiyo a kasa:


Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN