Type Here to Get Search Results !

Yanzu yanzu: An rufe 'white house' inda ake sha da sayar da barasa da Karuwanci a garin Koko da ke jihar Kebbi

An rufe white house inda ake sha da sayar da barasa da Karuwanci a garin Koko da ke jihar Kebbi


Shugaban karamar hukumar Koko/Bessse a jihar Kebbi, Alhaji Yahaya Bello, ya bayar da umarnin rufe wani gida da ke gudanar da mashaya ta sirri da gidan karuwai a garin Koko. Kamfanin dillancin labarai na Najeriya NAN ya ruwaito.

Bello, wanda ya bayyana hakan a ranar Laraba yayin da yake zantawa da manema labarai a Koko. ya ce ayyukan da ake gudanarwa a gidan da aka fi sani da ‘White House’, ya saba wa dokokin da ake da su.

“Mun ba da umarnin rufe "farar gida" inda ake sayar da barasa da sha da kuma ayyukan karuwai.

“Rufe gidan yana bisa dokar karamar hukumar da ta hana sayarwa da shan barasa, karuwanci da sauran munanan dabi’u a yankin,” inji shi.

Bello ya bukaci al’ummar yankin da su guji ayyukan da suka saba wa koyarwar addini da ka’idoji da dabi’u na al’umma.

Ya yi kira ga jami’an tsaro da masu ruwa da tsaki da su aiwatar da wannan umarni domin a rage munanan dabi’u da ayyukan ta’addanci a yankin.

A nasa bangaren Hakimin Koko Alhaji Muhammad Koko ya yabawa majalisar bisa rufe gidan.

Ya ce wannan odar ta zo a daidai lokacin da ya dace, ya kuma ce a kawar da duk wata munanan dabi’a ta zamantakewa da ta saba wa koyarwar Musulunci.

Hakimin ya ja kunnen matasan yankin da su rika gudanar da ayyuka masu inganci domin bayar da gudunmawar kason su ga ci gaban jihar. 

Post a Comment

0 Comments
* Please Don't Spam Here. All the Comments are Reviewed by Admin.

Top Post Ad

Below Post Ad

Hollywood Movies