Masu bikin Mauludi su 15 sun mutu bayan sun nutse a ruwa yayin da kwale-kwale ya kife da su a Sokoto

Masu bikin Mauludi su 15 sun mutu bayan sun nutse a ruwa yayin da kwale-kwale ya kife da su a Sokoto


Akalla mutane 15 ne aka ruwaito sun rasa rayukansu bayan da jirgin ruwan da suke ciki ya kife a kan hanyar ruwa da ke karamar hukumar Shagari a jihar Sokoto.

An tattaro cewa lamarin ya faru ne da yammacin Talata, 18 ga watan Oktoba, 2022, a lokacin da wadanda abin ya shafa za su je wani kauye da ke makwabtaka da su don halartar bikin Maulud Nabiy, domin tunawa da ranar haihuwar Annabi Muhammad. 

Shugaban karamar hukumar, Aliyu Abubakar Dantani, wanda ya tabbatar wa Daily trust faruwar lamarin, ya ce wadanda abin ya shafa sun fito ne daga kauyuka daban-daban.

“Su 25 ne suka shiga cikin kwale-kwalen a lokacin da jirgin ya kife amma an ceto 10 daga cikinsu da ransu, sun fito ne daga kauyuka hudu daban-daban, suka hadu a daya daga cikin kauyukan, daga nan ne suka shiga kwale-kwalen.” Inji shugaban. 

"Suna kan hanyarsu ta zuwa wani kauye ne domin gudanar da bikin Moulud na kowace shekara amma kwale-kwalen ya kife kafin su kai ga inda suka nufa.

Dantani ya ve hudu daga cikin mamatan sun fito ne daga kaiyen Gidan Raket, uku daga Gidan Dawa, bakwai daga Sabon Garin Sullubawa sai wata yarinya daga kauyen Tsohon Garin Sullubawa.

A kan alkawarin da Gwamna Aminu Waziri Tambuwal ya yi a shekarar 2021 na samar da rigunan ceto a kauyukan da ke kusa da karamar hukumar, shugaban ya ce "har yanzu ana kan hanya."

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN