A yau Litinin ne ake sa ran shugaban kasa Muhammadu Buhari zai tafi birnin Landan na kasar Birtaniya domin duba lafiyarsa.
Sanarwar ta fito ne ta hannun mai baiwa shugaban kasa shawara kan harkokin yada labarai, Femi Adesina, ta hanyar wani sako da ya wallafa a shafinsa na Twitter a safiyar ranar.
Cif Adesina, wanda shi ma ya fitar da sanarwar manema labarai kan ziyarar jinyar, ya ce shugaban zai dawo kasar ne mako na biyu na watan Nuwamba.
Shugaban ya soke shirin kaddamar da sabon rukunin fasaha da kere-kere na hukumar kula da fasahar kere-kere ta kasa (NASENI) domin jagorantar wani taron gaggawa na kwamitin tsaro na kasa.
Sai dai kuma ya yi tattaki zuwa garin Owerri na jihar Imo domin kaddamar da taro ga manyan jami’an ‘yan sanda kafin ya tashi zuwa Turai ranar Litinin.
RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI