Wani mutum da har yanzu ba a tantance ko wanene ba ya kashe kansa a unguwar Akute da ke jihar Legas bayan rabuwar sa da matarsa.
Shaidun gani da ido sun ce mutumin da matarsa sun samu rashin fahimta ne, kuma ta yanke shawarar ficewa daga auren. Domin ya fusata da shawararta, mijin da ya yi baƙin ciki ya yanke shawarar kashe rayuwarsa.
Wani mazaunin yankin mai suna Gallas Oluwaseyi wanda ya bada labarin a yanar gizo ya yi ikirarin cewa mutumin ya kai ‘yar sa wajen wani mai POS a unguwar su da ke titin Faleye kusa da mahadar Akute inda ya nemi a cire masa duka kudaden da ke cikin asusunsa. Ba a gama cinikin ba sai ya yanke jiki ya zube ya fara kumfa a bakinsa. Jama’a sun garzaya don ba shi manja, amma a karshe ya mutu.
Daga baya sun gano kwalbar maganin kwari mai suna Sniper a aljihunsa.