Wasu Hausawa sun yi hadari a Enugu, mutum 13 sun kone kurmus


Akalla fasinjoji 13 ne suka kone kurmus a wani hadarin motan da ya faru a kusa Four-Corners Enugu da misalin karfe 9 na daren jiya Lahadi, inji rahoton Vanguard.

An ruwaito cewa, motar mai daukar mutane 14 ta taso ne daga jihar Imo inda ta nufi jihar Adamawa a Arewacin Najeriya. Legit ta wallafa.

Rahotanni sun bayyana cewa, motar ta shigewa wata babban tirela ne kafin daga bisani ta kama da wuta.

Dukkan fasinjojin dake ciki sun kone kurmus kuma sun mutu face mutum daya da ya kone, shima ba a iya gane shi.

Yadda ya tsira daga hadarin

Wasu majiyoyi sun bayyana cewa, ya yi tsalle ne ya fice daga motar yayin da ta fadi, wasu kuwa suka ce mutanen dake gefe ne suka ciro shi daga cikin motar.

Vanguard ta tattarp cewa, mutumin da ya tsiran yanzu haka yana can kwance a asibitin koyarwa na jami'ar Najeriya ta Nsukka dake Ituku-Ozalla a jihar.

Da yake tabbatar da faruwar lamarin, kwamandan yanki na hukumar kula da haddura ta kasa a Enugu, Joseph Toby ya ce hukumar ta kan gargadi direbobi game da tafiye-tafiye cikin dare.

Toby ya kuma bayyana cewa, mutumin da ya tsira a yanzu haka yana asibiti yana karbar kulawar likita.

Ya kuma bayyana cewa, mutanen da hadarin ya rutsa dasu Hausawa ne, domin wasu Hausawa sun nemi a basu damar yi musu jana'iza.

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN