‘Yan bindiga sun tare babbar hanyar Zamfara bayan sun kai hari ofishin ‘yan sanda tare da sace wayoyin ‘yan sanda
A ranar Talata 25 ga watan Oktoba ne wasu ‘yan bindiga suka kai wa ofishin ‘yan sanda hari a unguwar Magami da ke Gusau a jihar Zamfara, inda suka sace wayar jami’an ‘yan sanda da ke bakin aiki.
Premium Times ta ruwaito cewa ‘yan bindigar sun isa unguwar ne da misalin karfe 3:40 na rana, inda suka nufi ofishin ‘yan sanda kai tsaye.
Wani dan jarida a yankin, Abdul Balarabe, ya ce mai yiyuwa harin ne hanyar da ‘yan ta’addan ke aikewa da sako karara ga hukumomin tsaro a jihar.
Balarabe ya ce;
"Daga abin da na koya ya zuwa yanzu, 'yan ta'addar ba su cutar da ko daya daga cikin 'yan sandan da suka samu a kan titin ba sai dai kawai sun tattara wayoyinsu da sauran kayayyaki masu daraja tare da yin barazana."
An kuma bayyana cewa, bayan tattara wayoyin jami’an ‘yan sandan, ‘yan ta’addan sun yi harbin iska, lamarin da ya haifar da hargitsi kafin su koma cikin daji.
Jaridar The Nation ta kuma ruwaito cewa wasu ‘yan bindiga sun kai hari kan babbar hanyar Funtua zuwa Gusau a jihar a ranar Talata.
Balarabe ya ci gaba da bayyana cewa an harbi wani matafiyi a kafa har sau biyu a yayin da direban motar da yake ciki ya ki tsayawa bayan da ‘yan bindiga suka umarce shi da ya tsaya.
Ya kara da cewa;
“Da misalin karfe 1 na rana a yau (Talata) ‘yan ta’addan sun fito da yawa tare da tare hanya. Wanda aka harba yana cikin motar da ta ki tsayawa.”
Dan jaridar ya kara da cewa lokacin da sojoji suka isa wurin suka share hanyar, 'yan ta'addan sun tsere ta hanyar daji suka tare Wanzamai zuwa Yankara sama da mintuna 30.