‘Yan sanda sun kama wani Nasiru Idris da ke karamar hukumar Sabon Birni a Sokoto bayan kama shi da katin zabe na dindindin 101.
Kwamishinan ‘yan sandan, Hussain Gumel, ya ce an kama wanda ake zargin ne a Sabon Birni a ranar 10 ga watan Oktoba, bayan samun sahihan bayanai.
Bayan kama shi, wanda ake zargin bai iya bayar da bayanin yadda ya samu PVCs ba. Gumel ya ce;
“An yi hasashen cewa masu wadannan katunan ba ‘yan karamar hukumar Sabon Birni ne kadai ba, za su iya fitowa daga sassan jihar saboda ba mu iya gano wadanda suka mallaki na’urar PVC ba.”
Kwamishinan ‘yan sandan ya kuma gaya wa jama’a, musamman wadanda katinan su ya bace ko kuma su zo hedkwatar rundunar su duba.
Ya kara da cewa hukumar ‘yan sanda za ta mayar da duk wasu katunan da ba a karba ba ga hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC) bayan wata daya.