Wata mata ta ba da labarin yadda mahaifinsu ya yi mata fyade tsawon shekaru har ta haifi ‘ya’ya 5 ga mahaifinta ISYAKU.COM

Wata mata ta ba da labarin yadda mahaifinsu ya yi mata fyade tsawon shekaru har ta haifi ‘ya’ya 5 ga mahaifinta

Ba ainihin hoton Aziza ba ne.

Wata mata ta ba da labarin yadda mahaifinsu ya yi mata fyade da yayunta tsawon shekaru.

Aziza Kabibi ta ce tun tana shekara 12 mahaifinta ya fara yi mata fyade tare da lakada mata duka kuma ta yi fatan ba a haife ta ba.

Ta bayyana cewa mahaifiyarta ta sani amma babu abin da ya taimaka.

An hana ta zuwa makaranta kuma an keɓe ta da danginta don kada ta buɗe wa kowa.

Ta kuma ce mahaifinta ya ce mata "Allah ne ya kaddara".

Ta ce tana so ta gudu daga gida wani lokaci amma yayanta da yayyenta suka hana ta.

Ta ce ta gane idan ta bar gida, mahaifinta zai fara wulakanta yayarta don haka ta zauna.

Mahaifinta ya yi alkawarin cewa idan ba ta yi kuka ba, ba zai taba ’yan uwanta ba, don haka ta daina korafi.

Sai dai daga baya ta gano cewa mahaifinta yana yi wa ’yan uwanta mata fyade.

A shekara 15, ta sami ciki da ɗan mahaifinta.

Daga karshe ta samu ciki har sau 5 ga mahaifinta da dukkan yaran da suma ‘yan uwanta ne mahaifinta ya haifa a gida.

Aziza da ‘ya’yanta, wadanda suma ‘yan uwanta ne

Gabaɗaya, mahaifinta ya haifa  'ya'ya shida gaba ɗaya daga cikin 'ya'yansa mata.

A wani rubutu na daban, ta yi hoton karar da mahaifinta ya yi a kotu bayan an fallasa shi.

Mahaifin matar wani Ba’amurke ne mai suna Aswad Ayinde.

Shi daraktan kiɗa ne da ya lashe lambar yabo ta Grammy, wanda ya shahara wajen jagorantar faifan bidiyo na waƙar Fugees mai suna "Killing Me Softly".

An yanke masa hukuncin daurin shekaru 90 a gidan yari a shekarar 2013 saboda laifin yi wa ‘ya’yansa mata 5 fyade.

Diyarsa, Azizah, yanzu tana raba labarinta a Instagram da TikTok kuma ta rubuta littafi game da shi.

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN