Attajirin Mawakin da ya yi shekara 4 bai rike kudi ba, ya rasa N850bn a cikin awa 24


Daya daga cikin manyan taurarin mawaka a Duniya, Kanye West ya tabbatar da rahoton da Forbes ta fitar a gaba da rasa dukiya da ya yi.

Jaridar The Nation ta gida ta rahoto Kanye West yana cewa ya yi asarar fam Dala biliyan 2 a rana daya. Hakan ya jawo ya fita daga sahun Biliniyoyi, legit.ng ta wallafa.

An zargi mawakin da nuna kiyayya ga yahudawa da bakaken fata, wannan ya jawo arzikinsa ya yi kasa, har ya sauka daga rukunin manyan Attajirai.

Tsohon mijin Kim Kardashian ya gamu da kalubale iri-iri sakamakon kalamansa. A makon nan kamfanin Adidas ya je yarjejeniyar da ya shiga da shi.

$1.5bn zuwa $400m

Tauraron da ake tunani ya mallaki fiye Dala biliyan 1.5 a asusun banki ya dawo yana da fam Dala miliyan 400 a sakamakon rasa manyan kwangiloli.

Forbes tace mawakin ya shaidawa wani 'dan kasuwa, Ari Emmanuel cewa duk da ya rasa Dala biliyan biyu a rana guda, yana nan da ransa, bai mutu ba.

Kanye West wanda akan kira da Ye ya fitar da jawabi mara batanci domin ya wanke kan shi.

A jawabin da ya fitar, West mai shekara 45 ya tabbatarwa ‘ri Emmanuel cewa yana mai kaunarsa har gobe, haka zalika Ubangiji ma yana kaunarsa.

Mutane sune mutum - West

West wanda ya shahara da wake-wake da gayu yake cewa mutane sune kasuwa, ba rumfuna ba.

“ARI EMMANUEL, NA RASA DALA BILIYAN BIYU A RANA DAYA KUMA GA NI DA RAI NA.

INA SON KA HAR YANZU. UBANGIJI YANA KAUNARKA. BA KUDI SUKA YI NI BA, MUTANE SUKA YI NI.

Shekara 4 bai taba kudi ba

Kwanakin baya an rahoto Kanye West yana cewa duk da irin dukiyar da ya mallaka, ya shafe kimanin shekaru hudu bai rike tsabar kudi da hannunsa ba.

Tauraron ya yi wannan bayani a wani bidiyo da wata mata ta dumfaro shi da kudi a hannunta.

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN