Type Here to Get Search Results !

Da dumi-dumi: Dan siyasa ya mutu a dakin Otal bayan ya yi lalata da wata mata - ISYAKU.COM


An tabbatar da mutuwar wani dan siyasa a jihar Ondo, Honourable Olanrewaju bayan ya yi lalata da masoyiyarsa a wani otel. Shafin labarai na isyaku.com ya samo.

Rahotanni sun bayyana cewa tsohon mai rike da mukamin siyasa a karamar hukumar Ondo ta Yamma, ya mutu ne a wani otel kuma ana zargin matar tana daure da ‘magun’ a ruhaniya wanda ya kai ga mutuwarsa.

Olanrewaju dan shekara 49 wanda ya tsaya takarar kansila ya mutu da misalin karfe tara na daren Laraba, 26 ga Oktoba.

Jaridar The Nation ta ruwaito cewa, masoyiyar tasa ta bayyana cewa mutumin ya fadi ne bayan ya yi wanka.

An ruwaito manajan otal din ya kira jami’an ofishin ‘yan sanda na Enu-Owa kafin a ajiye gawarsa a dakin ajiye gawa na asibitin koyarwa na Jami’ar Medical Sciences.

Kakakin rundunar ‘yan sandan Ondo, SP Fumilayo Odunlami, ya tabbatar da faruwar lamarin, ya kuma ce ana zargin lamarin ne na mutuwar kwatsam kuma ba bisa ka’ida ba.

Post a Comment

0 Comments
* Please Don't Spam Here. All the Comments are Reviewed by Admin.

Top Post Ad

Below Post Ad

Hollywood Movies