Siyasar Kebbi: Dan takarar Gwamna na jam’iyyar PDP ya yi alkawari mai ratsa zuciya ga jama'ar jihar Kebbi


Janar Aminu Bande mai ritaya, dan takarar Gwamnan jihar Kebbi a karkashin jam’iyyar People’s Democratic Party (PDP) a ranar Litinin ya yi alkawarin tafiyar da Gwamnati budaddiya idan aka zabe shi.

Da yake kaddamar da majalisar yakin neman zabensa a Birnin Kebbi, Bande ya ce takararsa na neman ci gaban jihar cikin hanzari ne.

NAN ta ruwaito Bande ya yi alkawarin yin adalci ga daukacin mazauna yankin ba tare da la’akari da addini, kabila da jam’iyya ba da nufin kai jihar ga wani matsayi mai girma.

Dan takarar ya bukaci majalisar yakin neman zaben da ta dauki sabon salo na yakin neman zabe inda kowane shugaba da daukacin mambobi za su gabatar da sashin zaben su.

Ya shaida wa taron yadda za a yi mu’amala da ‘yan siyasar da har yanzu suke son yin siyasar kudi a 2023.

“Idan sun kawo kudi ku karba, domin naku ne, amma ku tabbatar kun zabe mutumin kirki domin samun zaman lafiya, ci gaba da kawo canji a jihar Kebbi da Najeriya baki daya.”

Shugaban kungiyar yakin neman zaben, Alhaji Abubakar Shehu-Geda, ya yi kira ga mambobin kungiyar da su jajirce wajen ganin jam’iyyar ta samu nasara a zaben.

Ya yi nuni da jin dadin yadda dukkan jiga-jigan siyasa a jihar Kebbi sun hallara, don haka ya tabbatar da cewa PDP ta riga ta lashe zaben.

Shehu-Geda ya nemi goyon baya da hadin kan kowa da kowa domin samun nasarar zabe a fadin jihar.

Alhaji Bala Sani-Kangiwa, tsohon shugaban jam’iyyar APC a jihar ya ce: “Yanzu na gamsu cewa PDP ta riga ta lashe dukkan mukaman zabe duba da irin jiga-jigan da na gani a nan.

"Duk da haka, ina so in yi kira da dukkan ku da ku koma gida ku shawo kan jama'ar ku don su zabi jam'iyyarmu ta PDP a dukkan mukamai na zaben 2023."

A nasa bangaren, kwamishinan hukumar kula da halayya ta tarayya mai wakiltar jihar Kebbi, Alhaji Abubakar Atiku-Bubu, ya bukaci dukkanin jam’iyyun siyasa da su gudanar da yakin neman zabensu cikin mutunci.

Ya ce sun yanke shawarar kafa tanti da PDP ganin yadda tsohon Janar din ya kasance a jam’iyyar ne domin ya kawo hayyaci da kuma canjin da ake so a jihar Kebbi.

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN