Majalisar Musulmi ta kori wani babban Limami daga mukaminsa, duba dalili
Majalisar Musulmi ta Ikare ta kori babban limamin Masallacin Ikare, Sheikh Abubakar Muhammed Abbas, kamar yadda wata wasika mai dauke da kwanan watan Oktoba 10, 2022 ta tabbatar.
An cimma matsayar ne a wani taro da aka yi a ranar 9 ga Oktoba, 2022. A cikin wasikar mai dauke da sa hannun shugaban majalisar, Adewale Jimoh Abayomi da sakatare, Alhaji R. Ayeigbusi, ta bayyana cewa Okukare na Ikare, Oba Saliu Akadiri Momoh IV. amince da shawarar.
Sai dai jaridar The Nation ta ruwaito cewa kungiyar Limamai da Alfas a jihar ta yi watsi da korar Sheikh Abbas.
Kungiyar ta ce matakin da ta dauka ya yi daidai da matakin da Gwamnatin jihar Ondo ta dauka tare da warware rikicin al’ummar Musulmin Ikare.
Rubuta ra ayin ka