MAGANIN CIWON YATSA NA DAN KANKARE
Wannan ciwon yatsane da ake alakantawa da miyagun yawu na mutane,waton kambun baka kenan wanda idan mai kambun baka ya ga wani abu a jikinka na wata baiwa ko fasaha ya yi magana to nan take wani ciwo zai iya tsira a jikinka. Wanda wannan ciwon yatsa mai azabar zafi yana daga ciki. Wasu kuma a kan jarrabe su ne da yin ciwon a duk shekara ta Allah.
Maganin shi a nan, shi ne
A nemi ganyen lalle tareda ganyen kaikayi komawa kan masheqiya
Sai a dake su a kwaba da man kadanya kada a saka Vaseline man kadanya kawai za a saka a kwaba garin
Sai a wanke yatsan da ruwan zafi sosai, sai a shafawa yatsan dukan shi, bayan ya wuni a sake cirewa a wanke da ruwan zafi kuma a sake shafa wani a kan yatsan, haka za a yi tayi kamin kwana uku insha Allahu za a ga abun mamaki cikin Dan gajeren lokaci yatsan zai warke.
Credit: Engr Ibrahim Saidu Uba
Rubuta ra ayin ka