Yan sanda sun kama wani mutum da ake zargi da yi wa yarinya ‘yar shekara 16 fyade a wani kabari a Arewacin Najeriya


Jami’an ‘yan sandan jihar Gombe sun kama wani mai suna Reuben Azariah da ke unguwar Tarmana a karamar hukumar Kaltungo bisa zargin yi wa wata yarinya ‘yar shekara 16 fyade a kan wani kabari. Shafin labarai na isyaku.com ya samo.

Da yake tabbatar da kama shi ga manema labarai, Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, Mahid Abubakar, ya ce a ranar 2 ga watan Satumba da misalin karfe 8:30 na dare, an samu korafi daga mahaifiyar yarinyar cewa a ranar da misalin karfe 8 na dare, wanda ake zargin ya kai ‘yarta zuwa wani wurin kabari a cikin mahallinta kuma da karfi ya yi Mata fyade a saman kabarin.

Bayan samun korafin ne jami’an ‘yan sanda daga sashin Kaltungo suka kai dauki inda suka kama Reuben Azariya.

Mahid ya ce an kai wanda ake zargi da laifin zuwa babban asibitin Kaltungo domin duba lafiyarsa, inda ya kara da cewa ana kan binciken lamarin bayan an gurfanar da shi gaban kotu domin a yi masa shari’a.

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN