An tsinci gawar wani Malami a Sashen Accountancy na Auchi Polytechnic, Hassan Momoh a cikin momotars ranar Alhamis, 8 ga Satumba, 2022,
An tattaro cewa Momoh ya shiga makarantar koyon kasuwanci da ke Area 2 a Auchi Polytechnic a cikin shirin gabatar da lakca yayin da wasu daliban Accountancy suka lura cewa ya dauki tsawon lokaci fiye da yadda ya saba bai sauka daga motarsa ba.
Sakamakon haka daliban sun matsa wajen motar domin tambayar dalilin da ya sa bai fito ba sai suka same shi a sume.
Tare da taimakon jami’an tsaron makarantar an kai malamin Asibitin Polytechnic Cottage inda aka tabbatar da mutuwarsa.
An yi jana’izar marigayin a garinsu Yeluwa da ke Jattu-Uzairue a yammacin ranar Alhamis, 8 ga watan Satumba.