Saurayi ya shake mahaifinsa dan shekara 90 har Lahira, ya kwace katinsa na ATM ya binne shi a kangon gida, duba abin da ya biyo baya

Wani mutum ya kashe mahaifinsa dan shekara 90 don karbar katin ATM na banki


Yan sanda a jihar Kwara sun kama wani Hassan Ibrahim da laifin kashe mahaifinsa mai suna Sabi Ibrahim dan shekara 90 don kwace masa katin ATM dinsa.

Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, SP Ajayi Okasanmi ya bayyana a ranar Alhamis a Ilorin cewa wata Aishat Ibrahim ta kai kara wajen ‘yan sanda a ranar 5 ga watan Agusta cewa baba Ibrahim ya bata.

Ya kara da cewa bacewa kofur din sojan mai ritaya mai shekaru 90 ba zato ba tsammani ya haifar da tuhuma.

“Bincike kan lamarin ya kai ga kama Hassan, dan dattijon da ya bace.

“A yayin gudanar da bincike, wanda ake zargin ya amsa cewa ya yi wa mahaifinsa alluran kashe-kashen zafi da aka hada da wasu abubuwa, wanda ya yi haddasa masa rauni da dimuwa nan da nan.

“Ya yi hakan ne bayan ya dawo daga banki inda ya kai mahaifinsa ya sabunta katin ATM dinsa.

“Ya dauki mahaifin ne a kan babur wanda ya aro, ya kai shi wani gida da ba a kammala ba ya shake shi har lahira bayan mahaifin ya karbi sabon katin ATM.

"Bayan haka ya tona wani kabari mara zurfi inda ya binne mahaifinsa bayan ya kwace masa katin ATM," in ji Okasanmi.

Kakakin ‘yan sandan ya kara da cewa Hassan ya tsere zuwa jihar Kaduna inda ya fara janyewa daga asusun mahaifinsa da ya rasu. Ya riga ya cire Naira 59,000 kafin a kama shi.

Okasanmi ya kuma bayyana cewa Hassan ya sayar da babur din da ya aro kafin ya tsere zuwa Kaduna inda aka kama shi.

"An kwato katin ATM da babur din da aka sace," in ji shi.

Za a gurfanar da Hassan a gaban kuliya bayan cikakken bincike, kakakin ‘yan sandan ya tabbatar

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN