Yadda budurwa ta sheka Lahira nan take bayan mahaifinta ya kwada mata mari lokacin wata hatsaniya tsakaninsu

Yadda budurwa ta sheka Lahira nan take bayan mahaifinta ya kwada mata mari lokacin wata hatsaniya tsakaninsu



Wani mutum mai shekaru 58 na fuskantar tuhumar kisan kai bayan da ya 'mari' 'yarsa mai shekaru 24 da haihuwa wanda ya kai ga mutuwarta a Mpumalanga, Afirka ta Kudu.
 

Wanda ake zargin, Fannie Mtshali ya bayyana a gaban kotun Majistare ta Ogies a ranar 12 ga Satumba, 2022.

Kakakin rundunar ‘yan sandan Mpumalanga, Brig Selvy Mohlala, a wata sanarwa da ya fitar ranar Talata, ya ce da misalin karfe 11 na daren ranar Asabar ne takaddama ta barke tsakanin Fannie Mtshali da ‘yarsa, Simphiwe, a Phola kusa da bankin Witbank. 

Rigimar ta kai ga yin arangama ta jiki a lokacin da Mtshali ya “mare ta” sai ta suma.

Mohlala ya ce an kira ‘yan sanda da jami’an agajin gaggawa amma da isarsu aka tabbatar da mutuwar budurwar. An kama Mtshali nan take bayan harin. 

An tsare Mtshali a gidan yari kuma an dage batun zuwa ranar 19 ga watan Satumba domin neman beli.

Da yake mayar da martani kan lamarin, kwamishinan lardin na SAPS a Mpumalanga, Laftanar Janar Semakaleng Daphney Manamela ya ce ya yi alhinin mutuwar yarinyar kuma ya ji takaicin yadda lamarin ya faru.

“Duk da cewa ya kamata a rika tarbiyyantar da yara, duk da haka ya kamata iyaye su guji yin amfani da tashin hankali, iyaye su ne ya kamata su kare ‘ya’yansu da iyalansu, har yanzu ana la’akari da cin zarafin jinsi a matsayin annoba kuma ba za mu iya rufe ido ba. wannan muguwar bala'i" Inji Janar din. 

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN