Da duminsa: Hatsarin mota ya rutsa da shugaban kasar Ukraine Zelensky (Bidiyo-Hotuna)

Da duminsa: Hatsarin mota ya rutsa da shugaban kasar Ukraine Zelensky


Shugaban kasar Ukraine, Volodymyr Zelensky ya yi hatsarin mota, kamar yadda kakakinsa ya bayyana. Shafin labarai na isyaku.com ya samo

Wata motar fasinja ta yi karo da motar shugaban kasar da kuma tawagarsa a babban birnin kasar Kyiv, in ji kakakin Sergii Nykyforov a wata gajeriyar sanarwa.

“Likita ne ya duba shugaban, ba a samu wani mummunan rauni ba,” inji shi.

An yi wa direban motar da ta yi karo da ayarin motocin magani a wurin, sannan aka tafi da su a cikin motar daukar marasa lafiya, kuma jami’an tsaro na ci gaba da binciken hatsarin


Hatsarin dai na zuwa ne bayan da shugaba Zelensky, mai shekaru 44, ya ziyarci birnin Izyum da aka kwato, wani muhimmin cibiya a arewa maso gabashin Ukraine, a ranar Laraba 14 ga watan Satumba.

Ya godewa sojojin da suka shiga cikin wani dauki-ba-dadi cikin gaggawa da aka kai wa ‘yan mamaya na Rasha, ya kuma sa ido a kan bikin kafa tuta.

Kalli bidiyon inda hatsarin ya afku a kasa...


Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN