Wani matashi mai shekaru 28 mai suna Umar Sale, ya rasu bayan da aka binne shi da rai a lokacin da yake tona yashi a wani rami a karamar hukumar Taura ta jihar Jigawa.
Lamarin ya faru ne a garin Majia da misalin karfe 2:3 na rana a ranar Talata 13 ga watan Satumba, 2022 lokacin da mutumin ke tono yashi da nufin gyara gidansa na laka wanda ruwan sama ya rusa wani bangare.
Kakakin hukumar tsaro ta farin kaya (NSCDC) reshen jihar Jigawa, Adamu Shehu, ya tabbatar da faruwar lamarin cikin wata sanarwa a ranar Laraba.
"Mahaifin 'ya'ya uku yana tono yashi daga wani rami mai nisan kilomita daya da garin Majia don gyara gidansa na laka wanda mamakon ruwan sama da aka yi a baya amma yashin da ke sama ya zame ya binne shi da rai," in ji shi.
“Kukansa na farko na neman agaji wasu mutane ne da ke noma a kewayen yankin suka ji suka yi gaggawar ceto shi.
“Abin takaici, ya mutu a wurin ne saboda nauyin yashi da kasa numfashi, inda aka tsinto gawarsa daga nan aka mika shi ga iyalansa domin yi musa jana’iza yadda ya kamata.
“A halin da ake ciki, bincike ya nuna cewa lamarin ba shi ne karo na farko da ya faru a cikin rami daya ba, domin an samu rahoton mutuwar mutane makamancin haka, don haka aka shawarci al’umma da su guji hako ko tona yashi daga ramin. Ya kara da cewa.