Wani mutum ya kashe iyayensa da kwarkwasa a Jihar arewa


An kama wani matashi dan shekara 37, Munkaila Adamu da laifin kashe iyayensa a karamar hukumar Gagarawa ta jihar Jigawa. Shafin labarai na isyaku.com ya samo.

Kakakin Rundunar ’Yan sandan Jihar, DSP Lawan Shiisu Adam, wanda ya tabbatar da faruwar lamarin a wata sanarwa da ya fitar, ya ce lamarin ya faru ne a ranar Alhamis 1 ga Satumba, 2022 a Unguwar Malamai da ke garin Gagarawa.

Shiisu ya bayyana cewa wanda ake zargin ya yi amfani da wata karamar katako inda ya kai wa mahaifinsa, Ahmad Muhammad da mahaifiyarsa, Hauwa Ahmadu, mai shekara 60 hari a dakinsu.

Muhammad, mai shekaru 70, shi ne shugaban kauyen na al'ummar. 

Kakakin ‘yan sandan ya ce wanda ake zargin ya kuma jikkata wasu mutane biyu a cikin al’umma.

Wadanda suka jikkata sun hada da Kailu Badugu mai shekaru 65 da kuma Hakalima Ahmadu mai shekaru 50 suna jinya a asibiti. 

Yayin da ba a iya gano dalilin aikata wannan aika-aikar ba, rundunar ‘yan sandan ta ce ta kama wanda ake zargin kuma ta fara bincike.

Adam ya ce sun kai mamatan zuwa babban asibitin Gumel inda aka tabbatar da mutuwarsu.

"An kama wanda ake zargi kuma an fara bincike." PPRO ya kara da cewa. 

A halin da ake ciki, Kwamishinan ’Yan sandan Jihar Jigawa, CP Aliyu Sale Tafida, ya bayar da umarnin a gaggauta mika shari’ar zuwa SCIID Dutse domin gudanar da sahihin bincike tare da gurfanar da mai laifin.

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN