An yankewa uwargidan tsohon shugaban kasar Malaysia, Rosmah Mansor hukuncin daurin shekaru 10 a gidan yari


An yankewa uwargidan tsohon shugaban kasar Malaysia, Rosmah Mansor hukuncin daurin shekaru 10 a gidan yari, bayan da aka same ta da laifin neman da kuma karbar cin hanci a lokacin mulkin mijinta na cin hanci da rashawa, mako guda bayan da aka daure shi a gidan yari saboda dimbin satar dukiyar jama’a. Shafin isyaku.com ya samo
.

An samu Rosmah da laifin neman ringgit miliyan 187.5 (dala miliyan 42) da kuma tuhume-tuhume biyu na karbar ringgit miliyan 6.5 (dala miliyan 1.5) tsakanin shekarar 2016 da 2017 don taimakawa wani kamfani wajen tabbatar da wani aikin samar da hasken rana ga makarantu a tsibirin Borneo.

Kotun ta yanke mata hukuncin zaman gidan yari na shekaru 10 a kan kowane tuhume-tuhumen, da za a yi mata a lokaci guda, da kuma tarar ringgit miliyan 970 (dala miliyan 217). Za a bar ta ta ci gaba da zama cikin 'yanci kan beli har sai an daukaka kara zuwa manyan kotuna.

Alkalin babban kotun Mohamed Zaini Mazlan ya ce masu gabatar da kara sun tabbatar da babu shakka cewa Rosmah ta nemi cin hanci da rashawa tare da karbar kudi a matsayin tukuici. Ya ce kariyar da ta yi “musu ce kawai, ba tare da sahihin shaida ba.”

Tun da farko dai Rosmah ta yi roko mai ratsa zuciya daga akwatin wadanda ake tuhuma a cikin Kotu, tana mai cewa ta yi bakin ciki kuma ta ji ba a yi mata adalci ba. Ta ce ba ta taba neman ko sisin kwabo ba a lokacin da take jagorantar gidauniyar agaji a lokacin da take matar Firai Minista.

Ta kuma koka a matsayin zalunci a siyasance al'amuran da suka kai ga daure Najib da azabtar da danginta.

“Ban ma san kudin aikin ba. Don haka gaskiya kawai nake fada ba komai ba sai gaskiya, in dai haka ne na mika wuya ga Allah.

Daga baya lauya mai kare Jagjit Singh ya shaidawa manema labarai cewa adadin tarar ita ce mafi girma da aka taba samu a tarihin Malaysia. Ya ce Rosmah ta kadu kuma ranta ya baci, kuma suna shirin daukaka kara zuwa manyan Kotuna.

A karkashin dokar, kowane tuhuma yana da hukuncin daurin shekaru 20 a gidan yari da tarar sau biyar na cin hancin da aka nema da karba.

Hukuncin nata ya zo ne bayan da maigidanta Najib ya fara zaman gidan yari na tsawon shekaru 12 a ranar Talatar da ta gabata, bayan da ya rasa nassara a daukaka kara da ya yi a daya daga cikin kararraki biyar da ake tuhumarsa da su da suka shafi satar biliyoyin daloli na 1MDB.

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN