Tinubu: Kiristocin Arewa sun bayyana abin da za su yi wa dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC

Tinubu: Kiristocin Arewa sun bayyana abin da za su yi wa dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC 


Matsalolin da jam’iyyar APC mai mulki ke fuskanta dangane da tikitin takararta na Musulmi da Musulmi ba za su kau nan ba da jimawa ba kungiyar Kiristocin Arewa ta sake jaddada matsayinta, inda ta ce ba za ta ja da baya ba.

Dandalin yana karkashin jagorancin tsohon Kakakin Majalisar wakilai, Yakubu Dogara, kamar yadda jaridar Vanguard ta ruwaito.

A cewar Dogara, dandalin zai gana da daukacin ‘yan takarar shugaban kasa, a sassan jam’iyya, sannan za su fito da zabin da suka dace.

Hakan ya biyo bayan ganawar da Dogara ya yi da shugabannin addinin Kirista na jihohin Arewa 19 da kuma babban birnin tarayya Abuja a ci gaba da tuntubar su gabanin zaben 2023.

An tattaro cewa baya ga tsohon Kakakin, sauran wadanda suka halarci taron sun hada da tsohon Sakataren Vwamnatin tarayya, SGF, Mista Babachir Lawal; Sanatan APC daga jihar Adamawa, Elisha Abbo; tsohon mataimakin Gwamnan jihar Kogi, Simon Achuba da dukkan shugabannin kungiyar Kiristoci ta Najeriya CAN daga jihohin Arewa 19 da kuma babban birnin tarayya.

Da yake tabbatar da taron a wani sako da ya wallafa a shafin sa na Twitter, a jiya, Dogara ya rubuta:

“#NigeriaDecides2023: Ana ci gaba da gwagwarmayar tabbatar da adalci. A yau (jiya), mun gudanar da taron tuntuba da shugabannin addinin Kirista daga jihohin Arewa 19 da kuma babban birnin tarayya Abuja kan tsarin da Najeriya za ta dauka a shekarar 2023.”

A nasa bangaren, shugaban CAN na jihar Kaduna, Rabaran John Hayab, ya ce:

“Taron ya samu halartar manyan shugabannin CAN daga Arewa sai jihar Katsina. Muna cewa ba gudu ba ja da baya kan matsayarmu a kan tikitin jam’iyyar APC Musulmi da Musulmi.”

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN