Malama Fatima Sani, mahaifiyar Abbas Abubakar da ake zargin wasu matasa sun kashe shi a Badariya na garin Birnin kebbi, ta ce ita kam bata yafe kisan da aka yi wa danta ba. Shafin labarai na isyaku.com ya ruwaito.
Rahotanni na cewa ana zargin wasu makwabta a Unguwar Badariya, Birnin kebbi sun yi wa Abbas dukar ajali ranar 19 ga watan Satumba 2022 bisa wani zargi da bayanai ke hasashen rashin ingancinsa.
Fatima ta ce: "Bayan sun sa Abbas cikin gida sun yi masa kisar gilla, bayan hukumar Yan sanda tana nan tana bincike, sai ga wasu sun ziyarce ni. Da Sarkin Gobi, da Sarkin Malamai, da Limamin Masallacin Jokolo a nan garin Birnin kebbi, da sauran tawaga.
Sun zo sun yi mani gaisuwar sun ba ni hakuri matsayin in yafe, ni kuma na ce masu Wallahi ban yafe ba kuma bani da niyyar in yafe masu.
Don haka ina mika kuka na ga mai girma Gwamnan jihar Kebbi Atiku Bagudu, shi taimaka min ya shiga cikin wannan lalura.
Shi kwato min hakki na a matsayj na, na mamar Abbas da aka yi wa kisar gilla.
Ina kai kuka na ga Alkalin Alkalai na jihar Kebbi, da duk wanda ke fada a ji, su taimaka mini, su tausaya mini kan wannan lalura".
Latsa kasa ka kalli bidiyon jawabin mahaifiyar marigayi Abbas: