Maganin dafin cizon machiji da na guba
Akwai macizai da yawa wadanda ke da zafin dafi wadanda idan suka sari mutum kai tsaye sai lahira.
Idan aka samu wanda maciji ya sara ko kuma wanda ya sha guba kawai a samu sassaken iccen kashu (Cashew) sai a saka a baki a tattauna shi idan aka tattauna sai a hade ruwan amma kada a hadiye tukar sassaken. Yin hakan zai narkar da dafin nan take ko da Mesa (anaconda) ce ta sare mutum. Hakan za'a narkar da dafin cizon macijin.
Kuma ana iya samo sassaken iccen kashu din a ajiye a gida ko gona ko ma a wajen aiki idan irin hakan ta faru sai a dauko wannan sassaken iccen kashu din a saka a cikin ruwa idan ya dan jika sai a tattauna a hadiye ruwan a zubar da tukkar insha Allahu za'a dace.
Allah ya kara yi mana kariya daga sharin abin cutarwa.
Rubuta ra ayin ka