Rikici ya barke a jihar Arewa yayin da dalibai suka yi zanga-zangar raba yara maza da mata a makaranta
Wasu dalibai a jihar Bauchi sun gudanar da zanga-zangar nuna adawa da sabuwar manufar Gwamnatin jihar na raba ‘yan mata da maza a makarantu.
Daliban makarantun Sakandare daban-daban wadanda tun farko suka koma zaman karatu a ranar Litinin 19 ga watan Satumba.
Vanguard ta rahoto cewa kwamishinan ilimi na jihar Bauchi, Aliyu Tilde, ya ce Gwamnatin jihar ta kammala shirin raba dalibai maza da mata a makarantun sakandare a jihar.
Da yake magana da manema labarai a taron majalisar zartarwa ta jihar Bauchi, Tilde ya ce sabuwar manufar za ta kasance ne kawai a duk lokacin da kuma a duk inda ya yiwu.
A cewar Tilde, bukatar manufar ita ce magance tabarbarewar tarbiyya, wanda ya ce ya zama ruwan dare a tsakanin daliban makarantun sakandare.
Bugu da kari, makarantu masu zaman kansu za su yi la’akari da wannan shiri da kuma raba mazan da za su halarci ayyukansu na ilimi a wata cibiya da kuma mata a wata cibiya ta daban.
Rubuta ra ayin ka