Jigon siyasa ya sake fayyace gaskiyar yadda siyasar Kebbi ta tsakiya ke tafiya, ya wanke kanshi daga zargi


Jigon siyasa a garin Bunza da ke Kebbi ta tsakiya Alhaji Faruku Madawakin Bunza, ya sake fayyace gaskiyar yadda lamarin yake a tafiyar siyasar yankin Bunza. Shafin labarai na isyaku.com ya ruwaito.

A wani tattaunawa da shafin labarai na isyaku.com, Alhaji Faruku ya ce;

"Kada mutane su yi mana mumunar fahimta, ba wai muna cin mutuncin ubannin gidajenmu bane, muna tare da su kashi dari bisa dari. Ina son su gane cewa mafi yawan mutane da suka dauka idan zasu zo sukan dauki yan kudi kamar dubu 2 ko 3 su ba Yan bangar siyasa domin su dinga kuwa suna cewa sai wane-sai-wane!". 

"Amma su sani fa mafi yawancin wakilansu ba su da masu kuri'a a hannu. Akwai mutanensu wadanda suka dasa mun san su, sun bar jama'ar karkara suna can Abuja zaune tare da su". 

"To su sani fa abin nan da aka basu, basu ba kowa. Daga su sai 'ya'yansu. Yan kwangila da suka dasa a can domin su dasa wasu, basu dasa kowa ba a nan gida. 

A siyasance ina shiga wurare in gan jama'a kuma in bayar da abina goro. Amma sai mutane suka zo suka yi korafi cewa an bani kudi ban basu ba". 

"Ina son mutane su san cewa ba wanda ya bani ko N20, domin abina ne nake amfani da shi. Na fidi wannan ne don in kare kaina. Ina son wakilanmu da masu gidajen mu su san irin wadanda zasu takmaka wa domin su tallafa masu".


Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN