Siyasar Kebbi: Garuruwa 40 sun aike Wakilai a taron Gwade Ward Bunza domin samun alkiblar siyasa da za su bi, Madawakin Bunza ya magantu.. Isyaku News


Wakilai daga garuruwa akalla 40 sun gudanar da takaitaccen taron tuntuba, ci wa matsaya da kuma samun alkiblar da za su fuskanta a zamantakewa da siyasarsu karkashin Mazabar Gwade (Gwade Ward) a karamar hukumar mulki ta Bunza a tsakiyar jihar Kebbi. Shafin labarai na yanar gizo isyaku.com ya ruwaito.

Bisa bukatar al'ummar, jigo a sayisar al'ummar kuma jagora, Alhaji Faruku Madawakin Bunza ya amsa kira kuma ya halarci taron da aka gudanar ranar Alhamis 8 ga watan Satumba.

Bayan zana matsaloli da suke fuskanta na cikin gida, al'ummar sun kuma kalubalanci Yan siyasa tare da yin zargin watsi da su da bukatunsu a siyasance.


Malam Salihu Hakimi, daya daga cikin wadanda suka yi jawabi a wajen taron ya ce:

"A bangaren zancen siyasa, wanene daidai mu tunkara a saurari matsalolin mu tunda siyasa ta fara, muna da bukatu daban-daban. Muna buƙatar rijiyoyi an yi guda hudu amma har yau ba mu fara amfana da ruwansu ba, an bi duk yadda za a bi amma har yanzu jama'ar mu basu san ko akwai Gwamnati ba".

"Don  haka muna son mu yi shawara siyasa mai zuwa, minene daidai mu bi, minene mafita, su waye ya kamata su kai mu ga manya har manya su san kukan mu. Wannan shi ne shawara da muka dauka domin nan wurin Arauce, garuruwan nan basu tsoron kowa idan ranar kada kuri'a ne" inji Salihu Hakimi. 


Boyi kanen Mai gari Dan galadima ya yi jawabi dalla-dalla. Muhimmai daga ciki sun hada da:

1.Hadin kai tsakanin Arawa, Fulani,  Zabarmawa da sauran kabilu da ke Mazabar.
2. Duk Dan siyasa ko shugaba da baya ra'ayinsu suma ba za su yi nasa ra'ayi ba.
3. Shugabanni irin su Alhaji Faruku Madawakin Bunza da Hakimai masu gari, su ne ginshikin tafiyar jama'ar yankin. Kuma idan ba a sa su ba, ba za a gan sakamako mai kyau da ake bukata ba.
4. A yi wannan tafiya tare da matasa da shugabannin al'umma, tare da tuntubar Dattijai.

Daga karshe Alhaji Faruku Madawakin Bunza ya shaida wa manema labarai cewa:

 " Wannan taron namu ne duka, jama'armu sun zo sun same ni ranar Juma'a  kan cewa akwai matsaloli da suka dame su a siyasance Wanda ba a taimaka masu ba. Yan siyasa na ta yi masu alkawurra suna sabawa. Suka sa lokaci suka ce in zo in tabbatar da cewa akwai jama'a magoya baya wanda ke tafiya tare da mu. Mu Kuma yi yadda ya kamata, wa ya kamata a tallafa masa domin tafiyarmu ta yi nisa. Shi ya sa na sa wannan rana domin in basu shawara me ya kamata mu yi ko wa ya kama mu bi (A siyasance).


Nan Ward na Gwade ne, a karkashin Bunza, muna da rumfar zabe guda goma (10) mafi yawan mu da ke nan Yan siyasa ne masu kuri'a. Muna son Yan siyasa su je ward nasu su nemi jama'a a tabbatar da siyasarsu, su taho kasarsu su nemi jama'a . Muna da korafe-korafe, matsali sun yi yawa wanda ba a kula ba, ba a duba ba. Babu wani kulawa da aka bamu a gaskiya a siyasar nan. Amma muna neman mutane su hankalta su bamu hadin kai domin mu san wa ya kamata mu taimaka wa 100 bisa 100 a siyasance.".

Latsa kasa ka kalli bidiyo:

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN