Da dumi-dumi: Wata mata ta sake yin ikirari cewa ta haifi Annabi a jihar Kebbi, Kotu ta jefa ta Kurkuku tare da wasu mutum 3


Wata mata mai suna Binta Aliyu tare da mahaifinta Aliyu Isah, ranar Juma'a 9 ga watan Satumba, sun gurfana a gaban Kotun shari'ar Musulunci bayan Binta ta yi ikirarin cewa Dan da ta haifa mai suna Basiru wai Annabi ne. Shafin labarai na isyaku.com ya ruwaito.

Binta tare da Mahaifinta da wasu kannenta Abubakar Aliyu da Shafa Aliyu suna, daga cikin garin Kamba da ke karamar hukumar Dandi a jihar Kebbi, fuskantar tuhuma ne na yunkurin tayar da fitina da batanci ga addinin Musulunci.

Dan sanda mai gabatar da kara Sgt Faruku Muhammed mai.lambar aiki 493010 ya gaya wa Kotu cewa wadanda aka gurfanar sun hada baki ne domin su tayar da fitina da kuma batanci ga addinin Musulunci wanda ya ci karo da sashe na 60/ 336 na dokar Penal code na jihar Kebbi.

Sai dai bayan karanta wa Binta tuhumar da ake mata a gaban Kotu, ta amsa cewa haka ne domin dan da ta Haifa mai suna Basiru Sanusi dan shekara daya da wata takwas Annabi ne.

Sai dai Alkalin Kotun Basiru Umar Birnin kebbi, ya kalubalance ta cewa addinin Musulunci ya tabbatar cewa Babu wani Annabi da zai zo Duniya bayan Annabi Muhamadu SAW. Amma Binta ta kasa kawo kwakwaran hujjojin don kare ikirarinta.

Ta ce " Akwai ababe da yawa da ke nuna haka amma jama'a ba za su yarda ba"

Sai dai Alkali ya tambayi Binta ko ta yi imani cewa Annabi Muhammadu shi ne Annabin karshe, sai ta masa cewa eh. Alkali ya ce to yaya aka yi kuka sami wani Annabi ? Sai Binta ta ce haka Allah ya hukunta.

Alkali ya kawo aya tabbacin Annabi muhammadu shine karshen Annabawa, amma Binta ta kasa kaso hujja ko aya domin kare ikirarinta.

Binta ta gaya wa Kotu cewa

 "Na gan mu'ijiza tun kafin in haife shi, na ji magana da ban taba jin irin ta ba, an yi mani ishara da cewa zan haifi Annabi, duk da yake babu shi a Kur'ani babu shi a hadisi, ko kin fada ba za a yarda ba". Inji Binta

Alakali ya gaya wa Binta cewa 

"Idan  kin yi imani da addini ba lallai bane mafarkin ki ya zama gaskiya. Wane abu ne gareki na muijiza da zai tabbatar cewa ke lallai za ki haifi Annabi?'.

Ana cikin shari'a sai danta Basiru yana ta kuka a cikin Kotu, sakamakon haka Alkali ya ce duk Annabawa babu wanda ya dinga bata wa iyayensa rai, amma ga Basiru ya dami mutane da kuka a cikin Kotu. Sai dai Binta ta kasa cewa komai.

Daga karshe, Alkali ya yi umarni a tasa keyar Binta da mahaifinta tare da kannenta biyu zuwa Kurkuku har tsawon mako biyu sai a dawo da su domin ci gaba da shari'arsu.

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN