Type Here to Get Search Results !

Kotu ta soke takarar Sanata Adamu Aleiro na Kebbi ta Tsakiya


Wata babbar kotun Tarayya da ke zamanta a Birnin-Kebbi ta dakatar tsohon gwamnan jihar Sanata Muhammadu Adamu Aliero daga takarar dan majalisar dattijai na mazabar Kebbi ta tsakiya a jam’iyyar PDP. Shafin BBC Hausa ta wallafa.

Kotun ta kuma bayyana Alhaji Haruna Sa’idu Dan D.O a zaman halattaccen dan takarar sanata na PDP a zaben shekara mai zuwa.

A watan Yunin wannan shekarar ne Sanata Aliero ya sauya sheka zuwa PDP daga jam’iyyar APC mai mulki, yana ikirarin lashe zaben fidda gwani na mazabar da aka sake yi.

Sai dai, Alhaji Haruna Saidu da ke neman takarar ya yi fatali da wannan ikirari, inda ya kalubalanci lamarin a gaban kotu.

Hakan na zuwa ne kwanaki kalilan bayan da kotun ta hana Sanata Yahaya Abdullahi Argungu kasancewa dan takarar jam’iyyar PDP a mazabar Kebbi ta arewa.

Shi ma dai ya sauya sheka ne bayan kammala zaben fitar da gwani.

Post a Comment

0 Comments
* Please Don't Spam Here. All the Comments are Reviewed by Admin.

Top Post Ad

Below Post Ad

Hollywood Movies