Ma’aikatan kafafen yada labarai, sun fi fuskantar cin mutunci a Najeriya – Gwamna Mohammed
Gwamna Bala Mohammed na jihar Bauchi, a ranar Asabar din da ta gabata, ya ce ‘yan jarida da sauran masu aikin yada labarai ne suka fi fuskantar cin mutunci a Najeriya. Shafin isyaku.com ya samo.
NAN ta ruwaito cewa Mohammed ya bayyana hakan ne a Bauchi yayin da yake gabatar da sabbin motocin Toyota Hiece guda biyu ga ma’aikatan gidan jarida na gidan Gwamnati da kuma kungiyar ‘yan jarida ta kasa (NUJ) a jihar.
A cewarsa, masu aikin yada labarai a kullum suna fama da takura, kalubalen tattara labarai da wasu lokutan ma ba su da albashi1.
Ya kara da cewa ‘yan jarida sun sha wahala a shiru duk da cewa sun dora madubi ga al'umma .
Mohammed, wanda ya ce ya bayar da motocin ne domin nuna cewa aikin jarida da ‘yan jarida suna da mutunci, ya kara da cewa dole ne a mutunta su tare da karfafa musu gwiwa su yi aiki yadda ya kamata don samar da yanayi mai kyau.
Ya ce dole ne a ba wa ‘yan jarida daraja ta fuskar gudunmawar da suke bayarwa ga al’umma.