Kashe iyayena aikin jihadi ne – Mutumin da ya kashe iyayensa har lahira a Jigawa ya ce

Kashe iyayena aikin jihadi ne – Mutumin da ya kashe iyayensa har lahira a Jigawa ya ce


Mutumin da ya kashe iyayensa a jihar Jigawa, Munkaila Ahmadu ya shaidawa ‘yan sanda cewa ya aikata laifin ne a matsayin jihadi. Shafin isyaku.com ya samo.

A baya dai an ruwaito cewa, Ahmadu mazaunin kauyen Zarada-Sabuwa da ke karamar hukumar Gagarawa a jihar Jigawa, ya yi amfani da wata tabarya wajen kaiwa mahaifinsa, Ahmad Muhammad mai shekaru 70, wanda shi ne hakimin kauyen Zarada-Sabuwa da mahaifiyarsa Hauwa Ahmadu mai shekaru 60, yayin da kuma ya kai hari kan Kailu Badugu mai shekaru 65 da kuma Hakalima Ahmadu mai shekaru 50.

Da yake zantawa da manema labarai, Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Jigawa, DSP Lawan Shiisu Adam, ya ce wanda ake zargin ya amince da aikata laifin kuma bai nuna nadama ba.

Ya ce wanda ake zargin malami ne a wata makarantar Islamiyya da ke jihar, ba ya cikin wani shaye-shaye a lokacin da ya aikata laifin.

A cewar kakakin ‘yan sandan, wanda ake zargin ya ce iyayensa na sha’awar yi masa ba’a a duk lokacin da ya gudanar da ibadarsa.

“Shi malami ne a wata makarantar Islamiyya, mai hankali, ba a alakanta shi da shan kwayoyi, ko da goro.

A lokacin da ake yi masa tambayoyi, wanda ake zargin ya ci gaba da cewa, ya yi Jihadi, ya yi Jihadi, yana kan hanya, su (wadanda aka kashe) ba mutane ba ne,” in ji Kakakin ‘yan sandan.

Kakakin ya kara da cewa wanda ake zargin ya kara bayyana cewa iyayensa sun rika kiransa da mahaukaci.

“Ya shaida wa ‘yan sanda masu binciken wannan da wasu dalilai ne suka sa ya kashe su. Ya ce bai yi nadama ba, kuma a shirye yake ya fuskanci kowace doka,” ya kara da cewa

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN