Kamfanin Rarraba Wutar Lantarki ta Fatakwal (PHEDC), ya tabbatar da lantarki ya kama daya daga cikin ma’aikatansa lokacin da yake yanke wutar wani kwastoma da bai biya kudin wuta ba a Calabar.
An yi sa'a, ma'aikatan sun tsira.
Ma’aikacin PHEDC na gudanar da ayyukan lantarki ne a Junction Army, da ke kan babbar hanyar Muritala Mohammed a Calabar, lokacin da wutar lantarki ta kama shi.
Wani faifan bidiyo da ke yawo a yanar gizo ya nuna ’yan kallo sun taru a gindin sandar wutar lantarki domin kallon jami’in da lantarkin ya kama da ya kasa motsi a saman sandar.
Daga nan ne aka ga jami’ai suna ajiye tsani guda biyu wadanda ma’aikatan wutar lantarki biyu suka hau don isa wurin jami’in da ya ji rauni su dauke shi.
Mista Collins Igwe, Manajan yankin, PHEDC, ya ce an kai ma’aikatan asibitin sojojin ruwa domin yi musu magani.
An farfado da shi a asibiti kuma yanzu an sallame shi.
Wani abokin ma'aikatan wutar lantarkin ya ba da sabuntawa a Facebook. Ya ce ya yi magana da abokinsa kuma yana jin "karfi" bayan an sallame shi daga asibiti.