Kotun koli na Najeriya a ranar Alhamis ta tabbatar da Ademola Adeleke a matsayin zababben Gwamnan jihar Osun a hukunci da ta yanke. Jaridar Tribune ta ruwaito.
Lamari da ya kawo karshen jayayyar sharia dangane da kujerar Gwamnan jihar Osun.
Hukuncin Kotun koli na Najeriya shi ne jama'a ke wa lakabi da "hukuncin daga ke sai Allah ya isa" domin dai babu wani hurumin sake wani shari'a kan lamarin.
RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI