Daga karshe Buhari ya bayyana sirrin abin da ya sanya wa hannu da Jonathan da ya ba da damar gudanar da zaben 2015 cikin kwanciyar hankali

Daga karshe Buhari ya bayyana sirrin abin da  ya sanya wa hannu da Jonathan da ya ba da damar gudanar da zaben 2015 cikin kwanciyar hankali


Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ce yarjejeniyar zaman lafiya da ya rattabawa hannu da tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan da sauran ‘yan takarar shugaban kasa a tunkarar zaben 2015 ya taimaka wajen gudanar da zaben cikin kwanciyar hankali.

Shugaban ya bayyana haka ne a lokacin da kwamitin zaman lafiya na kasa (NPC) karkashin jagorancin tsohon shugaban kasa, Gen.Abdulsalami Abubakar (mai ritaya) ya ziyarce shi a fadar gwamnati da ke Abuja a ranar Alhamis, 29 ga watan Satumba.

Buhari ya bukaci ‘yan siyasar da suka rattaba hannu kan yarjejeniyar zaman lafiya da magoya bayansu da su yi biyayya ga abubuwan da ke cikinta a zaben 2023 mai zuwa.

Wannan tsari a cewar Buhari an yi shi ne da nufin ganin jam’iyyun siyasa da masu son tsayawa takara da magoya bayansu su gudanar da yakin neman zabensu cikin kwanciyar hankali.

Buhari ya ce:

“Lokacin da aka cimma yarjejeniyar zaman lafiya ta farko na da matukar muhimmanci idan aka yi la’akari da yakin neman zaben jam’iyyun siyasa a kasar.

“Shirye-shiryen da NPC ta yi abin yabawa ne saboda wannan yunƙurin zai tabbatar da kamfen ɗin da ya shafi batutuwa

“Ina fatan kashi na biyu na rattaba hannu kan yarjejeniyar zaman lafiya ta kasa da ke zuwa a watan Janairun 2023

“Za ku iya tunawa ni da shugaban kasa Goodluck Ebele Jonathan mun sanya hannu kan yarjejeniyar zaman lafiya ta kasa ta farko kafin zaben 2015

“Ina da yakinin cewa hakan ya taimaka matuka wajen samun nasarar zaben 2015 cikin kwanciyar hankali.

"Ina fata kwamitin zaman lafiya na kasa ya ci gaba da wannan muhimmin aiki.".

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN