MAGANIN CIWON HAKORI
CIWON HAKORI
A Sami Itacen Tumfafiya a dafa da jar kanwa a kurkura da dimin shi safe da yamma har kwana 3. Hakora za a warke,
KOGON HAKORI
A dibi audugar cikin kwallon tumfafiya a dangwali nonon ta kadan a sa cikin kogon, a rika yin haka lokaci-lokaci, kogon zai cike, (Amma fa akwai zafi)
TSUTSAR HAKORI
A tafasa saiwar tumfafiya a kurkura baki da dimin shi, sau 3 a rana kwana 2, Zaka Rabu da Ita,,
HAKORA MAI JINI
A dafa sassaken Tumfafiya da ganyenta a sa gishiri kadan, a kurkura baki da dumi-dumi sau 3 a rana kwan 1 zaayi, Hakora za su daina jini
WARIN BAKI
A dafa ruren Tumfafiya da kwallonta idan ruwan ya huce a sa a bin wanke baki (Brush) ana wanke bakin bayan an dan guntsi ruwan. Kayi ban kwana da doyin baki,
HASKEN HAKORA
A shanya furen Tumfafiya idan ya bushe a maida shi gari a hada shi da alaf kadan, a dangwala da Buroshi ko Asuwaki a wanke baki. Hakora za su yi fari tas,
DATTIN GORO KO HAYAKIN TABA
A dafa Furen Tumfafiya da Lemun tsami (Lime) a wanke baki da shi da a bin wanke baki (Brush). Dattin zai fita daga baki gaba daya.
Credit: #Maganin gargajiya