Asirin saurayi dan shekara 22 ya tonu bayan ya shiga Masallaci dakin Allah ya banka sata
Hukumar tsaron farin kaya ta Najeriya (NSCDC) reshen jihar Kano, ta kama wani Zahradeen Mukhtar, mai shekaru 22 da haihuwa, bisa zarginsa da yin barna tare da sace garkuwar taga a wani Masallaci.
Jami’in hulda da jama’a na hukumar DSC Ibrahim Idris-Abdullahi ne ya sanar da kamen a wata sanarwa da ya fitar ranar Talata a Kano.
Ya ce an kama wanda ake zargin ne dauke da wasu garkuwan tagar da ke babban Masallacin Dawakin Tofa.
“Wadanda ake zargin sun boye karafan garkuwar taga da suka sace a cikin wata katuwar buhu kuma suna kan hanyar kai su kasuwa sai jami’an NSCDC suka kama shi,” in ji Idris-Abdullahi.
A cewarsa, wanda ake zargin ya amsa laifin aikata sata kuma za a gurfanar da shi gaban kotu bayan kammala bincike.