Hukumar NCS ta kama haramtattun kayayyaki da kudinsu ya kai N61.5m a Kebbi


Hukumar Kwastam ta Najeriya (NCS) reshen jihar Kebbi, ta ce ta samu nasarar damke haramtattun kayayyaki da suka kai Naira miliyan 61.55 daga hannun wasu da ake zargin masu fasa kwaurin ne a Kebbi. Shafin isyaku.com ya samo.

Kampanin dillancin labarai na Najeriya NAN ta ruwaito cewa Kwanturolan hukumar kwastam a jihar Mista Joseph Attah ne ya bayyana haka a lokacin da yake zantawa da manema labarai kan ayyukan rundunar a ranar Alhamis a Birnin Kebbi.

Ya ce an samu nasarar kama su ne sakamakon jajircewar da rundunar ta yi na durkusar da ’yan kasuwa masu aikata laifuka a kan iyaka a jihar.

“Watan na Agusta ya kasance mai ban mamaki yayin da rundunar ta kara kaimi wajen yaki da masu fasa kwauri.

“Mun shiga manyan tarurruka tare da shugabannin gargajiya, siyasa da matasa da nufin samun fahimtar juna da bin ka’ida.

Attah ya ce, aikin da aka yi ya sa an kama jarkoki 824 na Man Fetur wanda ya kai lita 20,600 da buhunan taki 75.

Sauran sun hada da buhunan shinkafa guda 22, bali 128 na kayan sawa na hannu, jarkoki 22 na man kayan lambu, motar da aka yi amfani da su guda daya, buhunan sikari 54 da injin kwalekwalen gida guda takwas.

A cewar Attah, kayayyakin suna da jimillar harajin da aka biya naira miliyan 61,55.

Ya ce an kama mutum daya da ake zargin sannan kuma aka bayar da belinsa na gudanarwa.

A bangaren samar da kudaden shiga kuwa, Attah ya bayyana cewa rundunar ta samu kudi naira miliyan 38.2 a watan Agusta bayan sake bude iyakar Kamba.

Ya yi kira ga ‘yan kasuwa da su yi amfani da damar da aka sake bude kan iyakar Kamba domin gudanar da kasuwancinsu na kan iyaka.

“Haye ko yunÆ™urin wuce kaya ta kowace kan iyaka a Kebbi baya ga Kamba har yanzu haramun ne saboda manufar Gwamnatin Tarayya kan rufe iyakokin ta ci gaba da aiki,” in ji shi.

Attah ya bada tabbacin cewa rundunar zata rubanya kokarinta na saukaka harkokin kasuwanci da kuma hana fasa kwaurin kaya.

Ya kuma bukaci al’ummar jihar da su ba wa hukumar hadin kai domin ta yi musu hidima

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN