An tsinci jariri dan kwana daya da haihuwa a cikin kwandon shara
An tsinci wani jariri dan kwana daya da haihuwa a nannade cikin jakar laida polythene a cikin kwandon shara a wani wuri a jihar Legas.
SP Benjamin Hundeyin wanda shi ne kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, ya ce idan ba don a gaggauta gano jaririn ba, da jaririn ya mutu.
Ya bayyana cewa an ceto jaririn kuma yana cikin koshin lafiya.
Rubuta ra ayin ka